Neman Lahiya (#11726)

Sūnanka warkarwātā nē, yā Ubangijina, kuma tunāninka māgāni nē a garēni. Kusanci da kai nē bēgē na. Ƙaunarka ita cē abōkiyar tafiyāta. Rahamarka, ita cē warkēwāta, da madōgarāta dūniya da lāhira.
Bā shakka, kai nē mayalwaci, masani, mafi basīra.

-Bahá'u'lláh
-----------------------

Neman Lahiya (#11727)

Yā Allah, Ubangijina, ina rōƙon ka, a cikin tēkun warkarwarka, da hasken tarmāmuwar sāhiyar alhurmarka, da sūnanka wanda yake abun yabo ga bāyunka, da hazāƙar maganarka, da girman alhurmarka, kuma da rahamarka tabbatacciya tun kāfin abūbūwan da suke sama da ƙasa su tabbata, ka tsarkake ni da tsarkakakkun ruwan nan nāka waɗanda suke cike da rahamarka, ka kāre ni da kuskure, kāsāwa, tāshin hankali kō duk wani shirme.
Yā Ubangijina, kana ganin bāwanka nā rōƙō a ƙōfar alhērinka, sarƙafe ga igiyar karāmarka, yā maida duk gūrinsa a garēka.
Ina rōƙon ka yā Allāna, kar ka hana masa abunda ya rōƙe ka cikin dubun alhurmarka da hasken tarmāmuwar kyautatāwarka. Kai nē mai aikata abunda kake sō. Bā wani Allah illā kai, mai gāfartāwa, mayalwaci, karīmi.

-Bahá'u'lláh
-----------------------

Neman Lahiya (#11728)

Yā Ubangiji Allah maɗaukakin Sarki ! Ina rōƙon ka da sūnanka wanda ta garēshi ka ɗōra wanda shīnē kyāwonka, bisa kujērar īkon addīninka, sūnanka wanda da shīnē, kake sauyā kōmi, kuma kake haɗa kōmi, sūnanka dake hukunta kōmi, kake sallamar kōmi, kake kāre kōmi. 
Ina rōƙon ka kāre baiwarka wadda ta nēmi ɓūya garēka, kuma take nēman kāriyar wanda garēshi ka bayyana. Wannan baiwar tā mīƙa duka gūrinta da amincinta a garēka. Bā ta da lāfiya yā Allāna! Amma tā shiga ƙalƙashin inuwar iccen warkarwarka. Tā furgita, sai ta tsēro cikin birnin taimakonka, cūta tā kāda ta, sai ta nēmi ɗugon ruwan rangwamenka, tā tsōrata, sai ta zābura don ta iske ƙōramar kwanciyar hankalinka, tā ɗau zunubi, sai ta maida fuskarta wajen dakalin gāfararka. Ka rufēta a cikin īkonka, da mayāfin warkarwarka da alhurmarka, yā Allāna, abun ƙaunāta! Ka kōri ƙishirwarta da kāriyar rahamarka da ni’imarka. Ka kāre mata duk wata azāba, matsala kō cūta, kuma da duk wani abun da yake la’ananne a ganinka.
A gaskiya, kai nē wanda ka fi ɗaukaka bisa ga kōmi in ba kai da kanka ba. Hakīka, kai nē mai warkarwa, wanda ya isa ga kōmi, mai kārēwa, mai jin-ƙai har abada, mai rahama.

-Bahá'u'lláh
-----------------------

Neman Lahiya (#11729)

Yā Allāna, kai nē, wanda sūnayenka kē warkar da māsu cūta, kē sauko lāfiya ga masākai, kē ƙōsar da māsu ƙishurwa, kē kwantar da hankalin firgitattu, kē jāgōrar ɓatattu, kē ɗaukaka wanɗanda aka ƙasƙanta, kē arzita matalauta, kē wāyar da kan jāhilai, kē haskaka zukācen māsu duhun rai, kē sā murna ga māsu hushi, kē sā kuzāri ga zukācen da suka yi sanyi, kē karɓo hakin waɗanda aka zālunta. 
Da sūnanka nē yā Allāna, duk halittu suka rāyu, samāniya ta warware, ka halicci ƙasa, gizāgizai suke shāwāgi, ruwan sama suke zubōwa.
A gaskiya, duka wannan abūbūwa suna tabbatar da alhurmarka ga duka halitta. Don haka nē nike rōƙonka, da sūnanka wanda da shīnē ka bayyana ɗayantakarka, kuma ka ɗaukaka addininka sama ga duka halitta gabāɗaya, dōmin sūnāyenka mafi ɗaukaka, dōmin zātinka da ya fi ƙarfin yabo, ka sā a daren yau, daga gizāgizan rahamarka, ka sauko da ruwan warkarwā bisa wannan ɗan jārīrin da ka rāɓā garēka, cikin dūniyar da ka halitta. 
Yā Allāna, ka sā masa rīgar lāfiya da rāyuwa, yā abun ƙaunāta, ka kiyāye masa duk wata darūra kō cīwo, kuma ka kauce shi da duk abunda ka la’anta.
A gaskiya, mulkinka kē daidaita kōmi, kai nē karīmin wanda kē rāyuwa da kansa. Kuma ka tabbatar masa yā Allāna, da alhērin dūniya da na lāhira. Ƙudurarka da basīrarka sun isa ka aikata haka.

-Bahá'u'lláh
-----------------------

